Kungiyar Myetti Allah Ta Tabbatar Da Aukuwar Harin Kajuru

Kungiyar Myetti Allah ta Kajuru a jihar Kaduna ta tabbatar da cewa an kai wasu munanan hare-hare a karamar hukumar kuma adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar harin ya zarta wanda rahotanni suka bayyana.

Ardo Musa Aliyu, shine shugaban Kungiyar Myetti Allah na karamar hukumar Kajuru. Ya fadi cewa a ranakun Lahadi da Litinin da suka gabata ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai farmakin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 68 da hukumomi suka tabbatar da an yi jana’izar su, maharan sun kuma kwashe dukiyoyi da yawa tare da kona gidaje har ma da gawarwakin wasu mutanen da suka kashe.

A iya sanin Ardo Musa, ya zuwa yanzu babu wanda aka kama dangane da aukuwar wannan mummunan lamarin amma ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na can na kai-da-komo a yankin.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne rahotannin aukuwar hare-haren na karamar hukumar Kajuru suka bayyana, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da babban zabe a Najeriya wanda daga bisani hukumar zaben Najeriya ta INEC ta dage zuwa ranar 23 ga watan nan na Fabarairu.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Myetti Allah Ta Tabbatar Da Aukuwar Harin Kajuru - 4'02"