Alhaji Suleiman yana amsa tambayoyin manema labaru a garin Kaduna ne yayin da ya zargi sojoji da harbe masu shanu da sunan bincike.
Yace jami'an tsaro suna kai masu hari da wata manufa daban domin idan ana bincike inda aka yi fada ne kawai to da dama amma me ya kai bincike inda ba'a yi rikici ba. Ko a jiya akwai mutanen da aka kama, yaren Mbwase da guraye da layu da abun kone gidaje a yankin karamar hukumar Sanga.
Fulani da suke da dukiya a fili ba zasu tada rikici ba. Amma duk da haka an kona gidajen Fulani talatin da hudu. An harbe mutum biyu an kuma kama daya. A wurin da aka yi hakan ba rikici a keyi ba. Masu tada fitina suna tada fitina sabo da suna son ko wani matsayi ko kuma suna da wata manufa daban.
Shugaban yace al'umma Fulani na bukatar a zauna lafiya. A zauna da duk wadanda suke da ruwa da tsaki a lamarin a duba a gano umalubaisan matsalar. Duk wanda yayi laifi yakamata hukuma ta hukuntashi. Amma muddin mutum zai yi laifi ba za'a hukuntashi ba to akwai matsala.
Amma shugaban al'ummar 'yan kudancin jihar Kaduna Dr Ephraim Goje yace suna da dalilin zargin Fulani da hannu cikin hare-haren da ake kaiwa a yankin. Yace a cikin wadanda aka kama akwai tabbatacen Bafullatani a cikinsu. An kuma gano Fulani mazauna cikin kudancin Kaduna. Idan kuma ana shakka jami'an tsaro suna da shaidu da yawa. Yace idan an kama wani yakamata jami'an tsaro su bincika daga ina wanda aka kama ya fito.
Akan ko yarjejeniyar da suka yi da Fulani ta shiga kwandon shara ke nan sai Dr Goje yace bata shiga kwandon shara ba. Yace kodayake basu rubuta ba amma sun amince su dinga binciken duk wani abu da ya taso kuma a gano dalilin hakan. Akan wai sojoji suna kone gidajen Fulani Dr Goje yace shi babu abun da zai fada a kai. Yae amma akwai hanyoyin da zasu bi su kai koke-kokensu. To saidai duk lokacin da aka tura soja aiki zai yishi gadan gadan. Ko gidajen 'yan kudancin jihar sojoji suna shiga ba na Fulani ne kawai suke shiga ba.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5