Kungiyar Matasan Arewa (AYF) tayi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), data tabbatar da duk shirye shiryen da zatayi kafin sabuwar ranar zaben da ta tsayar, tana mai fadin cewa kara dage zaben ba zai yiwa yawanci ‘yan Nigeria dadi ba.
Shugaban kungiyar matasan Gambo Ibrahim Gujungu, a wata sanarwa yayi kira ga shugaba Jonathan da ya kori duk hafsosin kasar, soboda gazawar su da kuma rashin yi wa yan Nigeria aikin daya kamata.
Yace bai dace ba ace hafsoshin tsaron Najeriya, wadanda suke sane da zaben da aka shirya yi a watan Fabarairu, su bari sai da lokaci ya kure sannan su ce ba zasu iya tabbatar da matakan tsaro a lokacin zabe ba.
Sanarwar ta baiwa matasan arewa shawara da kada su yarda, yan siyasa suyi amfani dasu, ya kuma bukace su dasu zama masu hakuri ga hukumomi.
Shugaban kungiyar matasan Gambo Ibrahim Gujungu yace, “Muna rokon ‘yan Najeriya da kada su bari wata jam’iyyar siyasa ta tursasa musu, kota matsa musu lamba. Su kuma zabi mutanen da suka tabbata zasu zama shugabanni na gari. Najeriya zata ci gaba ne idan har an zabi shugabannin wadanda, a shirye suke, su yanke shawarar da za ta taimakawa mutane.”
Sanarwar ta kuma nuna damuwa kan wasu kalaman da wasu sanannun ‘yan Najeriya ke yi, musammamma, tsofaffin ‘yan yakin sakai na yankin Niger Delta, da suke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.