Kungiyar Masu Masana'antu Ta Mika Kokenta Ga Buhari

Kasuwar Wuse da ke Abuja a Najeriya. Janairu 30, 2018.

Kungiyar masu masana’antu ta najeriya wato MAN na cikin jerin kungiyyoyin da ke taka muhimmiyar rawa wajen habaka da ci gaban tattalin arziki Najeriya.

Baya ga cinikayyar kayayyakin da kamfanonin ‘ya'yan kungiyar ke sarrafawa, haka zalika, kamfanoni na zaman babban ginshikin samar da ayyukan yi ga miliyoyin ‘yan kasa.

Alhaji Sani Sale Birnin kudu, shi ne shugaban kungiyar ta masu masana’antu a jihar Kano kuma ya bayyanawa wannan fili ire-iren ababben da suke mafarkin gwamnatin ta samar domin inganta masana’antu.

"Babban burin masu masana'antu a arewa su ne, a samar da wutar lantarki, tituna, da hanyar layin dogo da janyo teku zuwa yankin arewa." Inji Alhaji Sani Hussuini birnin kudu, shugaban reshen jihar Kano kungiyar masu masana’antu ta najeriya.

Su ma ‘yan kasuwa da ke hadahadar kayayyakin Blouse na da makamancin wannan muradi ga sabuwa gwamnatin da shugaba Buhari zai kafa nan da watanni biyu masu zuwa.

"Fatanmu shi ne, mu 'yan kasuwa mu samu sauki fiye da yadda muke samu, wato mu samu canji (kudaden waje) da sauki." Inji Alhaji Dayyabu Salisu Sa’adu shugaban riko na kungiyarsu mai kula da yankin arewacin Najeriya.