Rashin kudaden daukan matakan inganta tsarin ciyarwa da na samarda magungunan kula da lafiyar kaji a gonaki na cikin matsalolin dake dabaibaye harkokin kiwon kaji a Jamhuriyar Nijar.
Matsalolin suka sa kungiyar manoman kaji ta fara nazarin hanyoyin jan hankulan bankuna domin su amince da baiwa manoman rance ko lamuni.
Adamu Kinba Abubakar shugaban kungiyar manoman kaji ya yi karin bayani akan bukatunsu. Yana mai cewa mutane sun dade suna kiwon kaji a kasar. Sun gogu. Sun samu ilimin sana'ar. Abun da ya rage masu shi ne su samu tallafi daga bankuna da masu taimakawa noma da kiwo. Suna kiran bankunan su taimaka masu da bashi domin su bunkasa sana'ar.
Habaka kiwon kaji ka iya bunkasa tattalin arzikin Nijar. Masu kiwon kajin sun ce yunkurin na da faida ta musamman ga ayyukan kare lafiyar jama'a saboda kowa a kasar na cin kaji yana kuma cin kwai.
Ofishin ministan bunkasa ayyukan noma da kiwo Audi Jallo Muhammad da ya wakilci gwamnati a taron na kiwon kaji ya yaba da tsarin wanda ya ce yana iya kawo karshen yunwa ko karancin abinci a kasar nan da shekarar 2021.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5