Kamar yadda yawan hare haren da tashin hankalin da ke da nasaba da kungiyar boko haram ke cigaba da takurawa jama'a musamman a arewa maso gabashin Najeriya, kungiyar masu buga Biredi da ke yankin arewacin sun yi wani gagarumin taro inda suka tattauna akan al'amura da dama wadanda ke da nasaba da tsaro, da kuma inganta sana'ar su domin lafiyar jama'a.
Kungiyar ta kaddamar da taron nata ne a Minna, jahar Neja. kuma a cikin abubuwan da kungiyar ta duba, sun hada da yadda masu buga biredin za su kara tsabtace shi domin kare lafiyar jama'a.
A cewar shugaban kungiyar Alhaji Tahir Adamu Bashar daga jahar kaduna, tunda an gane cewar yawancin rashin lafiyar da ke addabar jama'a na da nasaba da irin abincin da suke ci, kamar misali ciwon suga, da hawan jini. Shi ya sa muka ga yakamata mu jawo hankalin masu irin wannan sana'a domin fadakar da su akan illar wasu abubuwan da za su iya kara haifar da wannan matsala.
Shima Allahji Ibrahim Usman Bauchi tsohon masu Bredin ne a Najeriya kuma ya bayyana matsayin su akan sabuwar gwamnati Muhammadu Buhari musamman irin goyon bayan da suke wa gwamnatin da kuma alwashin bada kokari domin ganin cewa sun aiwatar da ayyukan su da sana'o'in su da gaskiya.
Ya kara da cewa suna neman taimakon gwamnati domin tabbatar da cewa an daina sa rogo a fulawar da ake yin Burodin da kuma daina anfani da wasu kayan hadin da ka iya shafar lafiyar jama'a.
Daga karshe sauran mahalarta taron daga arewa maso gabashin Najeriya, sun koka ne musamman dangane da yadda harkar tsoro ta hana su cigaba da gudanar da sana'ar su, mahalartan sun bayyana yadda suke bukatar sabuwar gwamnati ta taimaka wajan kara inganta harkar tsaro domin su samu su ci gaba da sana'oin su.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5