Kungiyar Manchester United Ta Shiga Idon Duniyar Tamola

'Yan wasan kungiyar Manchester United

Yawancin 'yan wasa da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool sun ce wannan ne karon farko da za su goyi bayan Manchester United a wani wasa.

Dan wasan Liverpool James Milner, shima yabi sahu da cewa wannan ne karon farko a rayuwarsa da zai goyi bayan babbar abokiyar hamayyarsu a kwallon kafa, kungiyar Manchester United sai dai dan wasan ya ce ba zai iya kallon wasan ba.

Magoya bayan sun ce za su goyi bayan Manchester United a wasan da za ta fafata da takwararta Manchester City a gasar Firimiya na bana karawa ta biyu.

Wasan zai dau hankali duk wasu masu sha'awar kwallon kafa a duniya, musamman a kasar Ingila wanda ake ganin sakamakon wasa shi zai hango kulob din da zai iya lashe kofin Firimiya na bana tsakanin Liverpool da Manchester City.

Liverpool ta ba Manchester City tazarar maki biyu a teburin Firimiya lig, inda take da maki 88, ita kuwa Manchester City tana da maki 86, yayin da ya rage saura wasanni uku a kammala gasar ta bana.

Liverpool tana bukatar Manchester United ta doke Man City, ko kuma ayi canjaras hakan zai bata karfin gwiwar lashe gasar a karon farko tun bayan shekaru 29 da suka wuce.

Shi kuwa a nasa bangaren mai horas da Manchester City Guardiola da zaran yayi nasara a wasan zai dare teburinne.

Manchester United kuwa ya zamo mata dole ta samu nasara a wasan da za'ayi a Old Trafford, matukar tana so ta shiga cikin jerin kungiyoyi hudu da zasu wakilci Ingila a gasar cin kofin zakarun Turai na badi, inda yanzu take mataki na shida da maki 64.

Za'a buga wasan wanda ya kasance kwantai ne na mako 31 a yau Laraba 24 ga watan Afirilu 2019, da misalin karfe takwas na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Chadi.