Wani kididdiga da akayi kan 'yan wasan da suke jinya cikin kungiyoyin da suke fafatawa a gasar Firimiya lig, na kasar Ingila ya nuna cewar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, itace tafi yawan 'yan wasa da suke fama da jinya a yanzu haka.
Manchester tana da 'yan wasa guda 10 da basa buga mata wasa da suka hada Eric Bertrand Bailly, dake fama da ciwon gwiwa ana sa ran sai ranar 21 ga watan Disambar 2019 kafin ya murmure.
Sauran kuwa sun hada da Anthony Martial, Phil Jones, Aaron Wan-Bissaka, Paul Pogba, Jesse Lingard, Mason Greenwood, inda ake saran zasu samu sauki zuwa 20 ga watan Oktoban nan da muke ciki.
Bayan haka akwai 'yan wasan da kungiyar tace zasu murmure nan da kwanaki biyu, wanda suka hada da Victor Lindelof, da yake fama da karamin jinya na bayansa.
Timothy Fosu-Mensah, da Diogo Dalot, ba'a bayyana ranar dawo warsu daga jinya ba.
Kungiyar ta Manchester United tana fama da rashin tabuka abun kirki a kakar wasan bana 2019/20, inda yanzu haka take mataki na 12 a teburin mako na Tara.
Wasu na ganin laifin maihoras da kungiyar ne Ole Gunnar Solkjaer, sabo da rashin gwanan cewarsa, shi kuwa kocin ya daura laifin ne kan 'yan wasan sa na rashin kokari da kwazo, a lokacin da suka shiga filin wasa a makon nan Newcastle United ta doke Manchester United daci 2-1.
Wasu rahotanni sun bayyana cewar da yuwar hukumomin kulob din zasu iya sallamar Solkjaer in har bai samu nasara a wasan da za suyi da Norwich City ba.