Kungiyar Manchester United Ce Ta Farko Da Kwallaye 1000

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta zamo kungiya ta farko data jefa kwallaye dubu daya (1,000) a wasannin premier league a cikin gida.

Anthony Martial ne ya jefa kwallo guda a yayin da kungiyar Red Devils ta lallasa kungiyar Everton da ci (1-0) a filin wasan Old Trafford ranar lahadin da ta gabata.

Wannan ya zo dai dai da ranar da kungiyar ta sama wani bangare a filin wasan suna Bobby Chalto.

Nasarar da kungiyar United ta samu ta daga ta zuwa ta biyar inda take ci gaba a hanyar su ta samun wuri a wassanin zakarun turai.

Kungiyar Arsenal ce ta zamo ta biyu da kwallaye dari tara da goma sha biyu (912), sai kuma kungiyra Chelsea ta zamo ta uku da kwallaye dari takaw da tasa’in da shidda (896).

Kungiyar West Ham na ci gaba da shirin zawarcin Odion Ighalo daga kungiyar Watford a kakar bana.

Dan wasan gaban na kungiyar Super Eagles ya ji dadin kakar wasannin da yayi da kungiyar Hornets inda ya jefa kwallaye har goma sha hudu 14 a wasanni 31.

A cewar rahotanni daga mujallar Sun ta tarayyar Turai, kungiyar Hammers ta dade tana kwadayin dan wasan mai shekadu 26, kuma yanzu haka sun kagara domin su sa shi cikin ‘yan wasan gaba a wasannin kaka mai zuwa.

Ighalo wanda ke da alaka da kungiyar Manchester United da Arsenal ya kai adadin kudin Ingila fan miliyan goma sha biyar.

Yanzu haka dai kungiyar West Ham nada ‘yan wasa biyar daga Afirka a cikin kungiyar, wato Cheikhou Kouyate, da Victor Moses, da Alex Song, da Diafra Sakho, da Emmanuel Emenike.