Kungiyar Maharba Ta kasa Da Kasa Tayi Taro

  • Ladan Ayawa

‘Yan kato da gora, da mafarauta na amfani da bindigogin gargajiya wajen zirga-zirga a birnin Yola.

Maharba na cikin ‘yan sa kai da suka taka muhimmiyar rawa na yaki da masu tayar da kayar baya na boko haram.

Kuma kamar yadda suka bayyana a wajen wannan biki na salala da suke yi shekara-shekara.

Maharban da suka fito daga jihohin arewa maso gabashinNajeriya sun lashi takobin ci gaba ne da wannan namijin kokarin da suke yi tare da fitar da bata garin dake neman bata musu suna.

Tun farko da yake jawabi mai masaukin baki kuma shugaban maharban jihar Adamawa Alhaji Mohammad Tola cewa yayi.

‘’Abin gargajiya na SALALAN maharba na jihar Adamawa dama baki daya na Najeriya ALLAH ya taimake mu, ALLAH ya bada hankuri.’’

Suk ace rookon ALLAH ne a samu kasa ta zauna lafiya.

Maharban suka e wannan bikin yana kara had kansu kuma suna ci gaba da bada gudun mowar su wajen samar da tsaro a sassan Najeriya daban-daban.

Ga Ibrahim Abdul Azeez da ci gaban rahoton 3’17

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Maharba Na kasa Da Kasa Tayi Taro 3'17