A Jihar Edo kungiyoyin lauyoyi ne da al’umma masu zaman kansu suke kokawa dangane da yadda harkokokin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a jihar, musamman a babban birnin jihar, wato, Benin, inda ko da rana tsaka ana fashi da makami tare da sace mutane ana garkuwa dasu domin karbar kudin fansa.
Su ma ‘yan kungiyoyin asiri ba’a barsu a baya ba a irin wanan aika aikan dake faruwa.
Dangane da hakan ne, Kungiyar lauyoyin jihar ta dauki matakin kauracewa duk wani zaman kotu kan satar mutane, fashi da makami da ta’arnakin kungiyoyin ‘yan asiri.
Barrister Asenegwu, shugaban kungiyar lauyoyin jihar, yace zasu ci gaba da kauracewa duk kararrakin har sai ‘yan sanda sun daina ba masu aikata laifukan kariya.
Alhaji Musa Saidu,shugaban ‘yan arewancin Najeriya mazauna yankin Niger Delta, ya tabattarda tabarbarewar sha’anin harkokin tsaro a jihar, inda yace ko cikin ‘yan kawanan nan an sace kanin karamin ministan kiwon lafiya tare da wani shahararren mawaki.
Amma Alhaji Baffati Sale, shugaban ‘yan Arewa mazauna jihar Edo, yace akwai tsaro a jihar saidai akwai rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar da kwamishanan ‘yan sanda. Yace matsalarsu bai kamata su shigar da ita a harkokin tsaro ba.
A halin yanzu kuma, wata kungiya ta ce zata kai koke ga Hukumar Kula Da Ma’aikatun Aikin ‘Yansandan Najeriya, akan cewa basu gamsu da aikin kwamishanan ‘yan sandan jihar ba, Haliru Gwandu.
Hukumar ‘yan sandan tace koken kungiyar tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama saboda daman tana binciken wasu kwamishanonin jihohi da dama kan zargin yin zarmiya.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5