Kungiyar Lafiya Ta Duniya Tace Rage Shan Sikari

Sikari

Kungiyar lafiya ta duniya tana kara kira ga mutane su rage yawan sikarin da suke sha.
Kungiyar lafiya ta duniya tana kara kira ga mutane su rage yawan sikarin da suke sha.

Wata kungiyar lafiya ta duniya dake Geneva tace daukar shan sikari na kulluyomin wanda ke kasan kashi biyar na abincin mutum kowacce rana, zai zama daidai, amma ta sake cewa yana da kyau rage shan kada ya wuce kashi 10 shima yana da kyau.

“Mu nemi kashi biyar idan zamu iya …… amma kashi 10 yafi tabbaci,” inji Dr. Francesco Branco, shugaban abinci da lafiya da kuma cigaba na kungiyar lafiya ta duniya.

Bisaga Branco, sikari zai iya zama sabon taba tawajen hatsari.”

Branco yayi gargadi gameda “sikarin da bamu gani.”

“Yawancin lokaci cikin abincin da muke ci ne, miyar da aka kara ga nama, chokali daya yana da ma’auni bakwai na sikari kuma yogot mai zaki yana da kimanin ma’auni shida.”

Kungiyar lafiya ta duniya tun tuni ta gargadi mutane su rage yawan sikarin su zuwa kashi 10 na kowacce rana wanda suke sha, amma kashi biyar din sabon shiri ne.

Sa wannan a hanyar aiwatarwa, kashi biyar zai zama kimanin chokali shida na sikarin kowacce rana; kwanon sikari na soda yana da kimanin kashi 10 na chokalin sikari.

Branco ya damu ne sosai kan shaye shayen zaki na yara.

“Matsakaicin mai aiki wurin saida abinci dake da sikari na soda … yana kusan kai ma’auni 30 na sikari a kowanne bayarwa,” inji Branco. “wannan ya rigaya ya wuce abinda ya kamaci yaro a kowacce rana.

Ya nanata cewa iyaye su rage yawan sikarin da ‘ya’yansu ke sha zuwa kashi biyar kawai, yaron bazai sami daudar hakori ba amma zasu zama da tsabta kuma zai yi wuya suyi girma fiye da kima.