Kungiyar ta shiga zanga-zangar neman biyan ta kudaden alawus na wata takwas da ‘ya’yan ta suka ce suna bin gwamnatin jiha wadda ta jefa su cikin matsanacin halin rayuwa da ba su iya biyan muhimman bukatunsu ba tare da kira ga gwamnati ta biya su hakkokinsu in ya so bayan haka ta rufe kulob na kwallon kafar idan ba zata iya gudanar da ita ba kamar yadda wasu da suka nema a sakaya sunansu suka bayyana.
Zanga-zanga na baya-bayan nan shine na uku a kasa da shekara daya,wanda sai Kungiyar ta tada jijiyar wuya ake biyansu wani kaso daga cikin alawus din da suke bin gwamnati, dalili da ya sa Muryar Amurka ta tambayi kwamishinan wasanni na jihar Taraba Rev. Gambo Nbafor matakan da suke dauka na magance matsalar wanda ya danganta da matsin tattalin arziki amma ya ce suna yin duk kokarin da ya wajaba.
Daga cikin masu asubanci don motsa jiki a filin wasannin zamani na Jolly Nyame da kungiyar kwallon kafar ta yi garkuwa da su na tsawon sa’o’I uku, akwai mai baiwa gwamnan jihar Taraba shawara kan harkokin labarai Silvanus Giwa da ya sha da kyar. Ya shawarci ‘ya’yan kungiyar su bi hanyoyin da tsari ya tanada wajen neman hakkokinsu.
Kungiyar kwallon kafa ta Taraba FC ta yi barazanar kauracewa wasanni na gaba idan gwamnati ta ci gaba da rike hakkokinsu a gasar rukunin kwararru na kwallon kafa ta kasa da yanzu ke zagaye na farko.
Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5