Kungiyar Kwallon Kafa Ta Wikki Tourist Tayi Wasu Canje-Canje

Haruna Abubakar

Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist dake jihar Bauchi a tarayyar Najeriya, ta nada sabon mai horas da 'yan wasanta mai suna Usman Abdallah Sheriff.

Usman ya maye gurbin Garba Ibrahim, wanda aka bukaci ya koma hukumar wasanni ta jihar (Bauchi State Sport Council) domin ci gaba da aiki a wani matakin.

Sauran canje-canjen da aka yi a kungiyar ta Wikki sun hada da maye gurbin mai horas da masu tsaron raga, mukamin da aka ba Haruna Abubakar, sannan aka ba Dantani Yahaya matsayin mai horoswa na biyu.

Su kuma wadanda aka karbi aikin a hanun su Bashir Sale, da Wada Jibrin, an bukaci su koma bakin aikin su a Hukumar wasanni ta Jiha.

A jiya Lahadi ne kungiyar ta Wikki Tourist ta hadu da rashin nasara a gidanta, inda kungiyar wasan Sunshine ta doke ta da ci 2-1 a gasar Firimiyar bana.

Kungiyar ta samu cikas a wasanni hudu da ta buga a gida, ta yi canjaros Uku, aka kuma sake doketa a wasanni Uku da ta buga a waje. Yanzu haka tana mataki na 14 daga kasan tebur.

Mai magana da yawun kungiyar Nasiru Abdullahi Kobi, ya ce sabon zubin da aka yi zai fara aiki nan take.

Kocin Usman Abdallah zai fara jan ragamar kulob din a yau Litinin 13 ga watan Janairu na shekarar 2020, a filin wasa na tunawa da Sir. Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, inda 'yan wasa zasu fara atisaye.