An kammala gasar firimiya lig ta shekarar 2018/19 a kasar Ingila, bayan an kwashe makonni 38 ana gwabzawa tsakanin kungiyoyin kwallon kafa ashirin.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ita ta lashe gasar a bana. Karo na biyu a Jere kenan domin a shekarar da ta gabata 2017/18, ita ta lashe wannan kofin.
Manchester City ta kammala wasanta a ranar Lahadi 12 ga watan Mayu 2019, tsakaninta da Brighton da Hove, inda ta lallasa ta da kwallaye 4-1 hakan ya bata maki 98 banbancin maki daya tak tsakaninta da Liverpool wace ta zo ta biyu da maki 97.
Wannan nasara da Manchester City tayi ta lashe kofin sau biyu a Jere. Karon farko kenan tun shekara 10 da suka wuce rabon da wata kungiya ta lashe kofi a jere.
Ita kuwa Liverpool Shekara 29 rabon da ta lashe kofin Lig a Ingila, haka kuma ba ta taba daukar kofin Firimiya Lig ba.
Kaftin din Manchester City Vincent Kompany ya jinjina da cin kofin Firimiya na 6 a tarihin kungiyar kuma na biyu a jere.
Jimillar kwallaye 31 aka jefa a raga a makon karshe na gasar Firimiya, a bana bayan haka an kafa tarihin cin jimillar kwallaye 1067 da ba a taba cin yawan kwallayen ba a kakar wasa daya, ya shafe tarihin da aka kafa a kakar 2011/12 inda aka jefa kwallaye 1,066.