Kungiyar ta kira taron majalisar kolinta gobe Juma'a domin ta daukin mataki kwakwara akan gwamnatin shugaba Buhari.
Tace na daya karin farashin man fetur da aka yi daga nera 85 zuwa 145 ba'a bi ka'ida ba domin akwai hukumar PPRA dake da hakkin kara ko rage farashin man fetur a cikin gida. Tace har yau gwamnati ta gagara hada hukumar.
Bayan wahalar rashin wutar lantarki da halin kakanikayi da gwamnati ta jefa jama'a ciki da wannene jama'a zasu ji, inji kungiyar kwadagon.
Manfetur ya shafi kowane haraka a rayuwar 'yan kasar. Saboda rashin wutar lantarki duk wani aiki da ake yi sai an sa man fetur cikin janareto koda ma aski mutum zai yi. Baki daya sha'anin tattalin arziki ya ta'allaka ne akan man fetur. Kungiyar ta kira gwamnati ta koma farashin da ta rushe sabon da ta fitar.
Kungiyar tace tunda an kara farashin man fetur farashin kaya da abinci zai tashi a duk kasuwannin kasar.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5