Tunda sanyin safiyar yau ne wakilan kungiyar kwadagon Najeriya aduk fadin kasar suka yi diran mikiya akan ofisoshin ma'aikatar samarda wutar lantarki saboda karin kudin wutar da aka yi.
Wakilan sun tabbatar cewa hada-hada irin na yau da kullum basu gudana ba a duk fadin kasar lamarin da ya sa wadanda suke je sayen katin wuta kokuma biyan kudi basu samu yin hakan ba..
Kungiyar ta hana ma'aikatan shiga ko fita daga ofisoshinsu.
Wani daga cikin shugabannin kungiyar kwadago yace sun dauki matakin ne domin tilastawa kamfanonin wutar lantarki su janye karin da suka yi daya ga wannan watan domin a wasu wuraren babu karin samun wutar lantarki. Yace kara kudin ba adalci ba ne a irin yanayin da mutane ke ciki.
Wasu da aka zanta dasu sun ce kafin a kara kudin wuta kamata ya yi a samu karin wutar. Suna cewa shi talaka da yake fama da yadda zai samu abinci yaci ba shi ne za'a karawa kudin wuta ba. Suna kiran gwamnati da ta yiwa Allah ta ji tausayin wahalar da talaka ke sha ta mayar da kudin wuta yadda yake da can.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5