Kungiyar Kwadago Ta Rufe Ayyukan Gwamnatin Jihar Imo

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

Yanzu haka dai kusoshin kungiyar Kwadago ta Najeriya sun tattaru a jihar Imo da nufin yiwa gwamnatin jihar taron dangi.

Kusoshin kungiyar Kwadago ta Najeriya, yanzu haka sun taru a Owerri babban birnin jihar Imo, domin rufe duk ayyukan gwamnatin jihar biyo bayan korar ma’aikata da gwamnan jihar Rochas Okorocha yayi.

Mako biyu da ya gabata gwamnan jihar yayi alkarin ba zai rage ma’aikatan jihar ba, zai kuma biya su hakkin su. Sai daga baya aka fitar da sanarwar an sallami ma’aikata har kusan dubu biyar.

Yanzu haka dai an toshe hanyoyi a birnin, an kuma bukaci a rufe tashar jirgin sama domin hana zirga zirgar jirage.

Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina yayi kokarin jin ta bakin gwamna Rochas Okorocha, amma abin ya ci tura, kuma abin jira a gani shine yadda wannan danbarwa zata kasance.

Don karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Kwadago Ta Rufe Ayyukan Gwamnatin Jihar Imo - 1'52"