Cikin sanarwa da shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ko NLC ya fitar Kwamred Ayuba Wabba, yace 'yan kwadagon kasar suna goyon bayan binciken badakalar kwangilar karya ta sayowa sojin Najeriya makamai da gwamnatin da ta shude ta yi..
A kwangilar bogin dai wasu 'yan tsiraru suka wawure dubban miliyoyin nera na kin kari kamar hauka.
Sakataren tsare tsare na kungiyar Kwamred Abayo Toro yace kwanan nan suka samu labari cewa wajen dalar Amurka biliyan biyu da digo daya aka samosu daga jami'an gwamnati da suka yi sama da fadi dasu. Dama an yi niyar sayowa sojoji kayan aiki ne da kudaden amma aka salwantar dasu ta wata hanya.
Kungiyar kwadago ta jinjinawa shugaban kasa Muhammad Buhari. Yace koda shugaban bai yi komi ba amma ya kwato kudaden da aka sace ya kayatar.
Akan abun da yakamata a yi domin shawo kan cin hanci a Najeriya Abayo Toro yace kungiyar kwadago tana goyon gwamnati dari bisa dari a tsayar da hukunci kisa akan duk wanda aka tabbatar ya wawure kudin jama'a.
Shi ma Sanata Shehu Sani yace su wadanda suka wawure kudin sayen makamai sun mai da tashin hankali da kashe-kashe hanyoyin cin riba da samun makudan kudi. Kama manyan jami'an tsaro da aka yi shi ne daidai domin a bincikesu domin su fada ma duniya gaba daya abubuwan da suka dinga yi. Yakamata a fadada binciken ya hada da wasu jami'an kasashen waje.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5