A wurin taron kungiyar ta karkata hankalinta ne akan yadda gwamnatin Kamaru ke gudanar da ayyukanta tsakaninta da al'ummar kasar musamman wajen samar wa al'ummar kasar abubuwan more rayuwa saboda haki ne da ya rataya akan gwamnati..
Taron ya duba irin abubuwan da kungiyar ta yi a shekarar 2015 da wadanda zata yi a shekara mai zuwa. Taron ya bata zarafin duba nasarori ko kasawa da ta fuskanta.
An gudanar da taron ne a birnin Yaounde inda ta duba sha'anin ilimi da irin hubasar da gwamnati ta yi ko bata yi ba. Akwai kuma sha'anin wutar lantarki, noma da kiwo da tanadar da ruwa mai tsafta da kiwon lafiya da yadda ake gudanar da sha'anin shari'a a kasar gaba daya.
Haka ma kungiyar bata bar maganar tsaro a baya ba kasancewa kasar tana fama da 'yan Boko Haram masu tada kayar baya musamman a arewacin kasar.
Kungiyar ta duba yadda gwamnatin Kamaru ke barin al'ummarta fadan albarkacin bakinsu da kuma 'yancin jaridu da watsa labarai bada wata tsagwama ba.
Firayim Ministan kasar yace kasar Kamaru ta shiga Majlisar Dinkin Duniya ne bayan ta cika sharudan kare hakin bil Adam.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5