Kungiyar kare hakin bil’adama ta Human Rights Watch ta fitar da rahoton ta na shekarar 2018, inda ta yi kira ga shuwagabanni su yaki 'yan siyasa masu ra'ayin kama karya dake rabewa da guzuma domin su harbi karsana.
Shekarar da ta gabata na nuna muhimmancin ture barazanar da 'yan siyasa masu neman matsayi da manufofin su na batanci ga al’umma, a cewar Kenneth Roth babban darectan kungiyar kare hakin bil’adama ta Human Rufgts Watch.
Roth ya zargi masu ra’ayin mulkin mallaka da neman hanyoyin da za su maye gwamnatin da aka zaba bisa tafarkin mulkin dimokradiyya wadanda suke da kayyadadden dama da gudanar da harkokin mulki bisa doka.
Rohoton ya zabe kasar Faransa a zamar zakaran gwajin dafin misalin bijirewar daya samu nasara, inda shugaba Emmanuel Macron ya jagoranci yakin neman zaben sausaucin goyon bayan turai akan mai ra’ayin rikau Marine Le Pen.