Kungiyar Izala Reshen Jihar Oyo Ta Tallafawa Zaurawa, Marayu da Gajiyayyu

  • Hasan Tambuwal

Shugaban Kungiyar IZALA Na Kasa Shaikh Abdullahi Lau

Reshen jihar Oyo na kungiyar IZALA ya samu kudi daga wasu rassansa biyar kimanin Nera miliyan uku da sama da dubu dari tara da ya rabawa zaurawa da marayu da gajiyayyu a jihar

Shaikh Salisu Abdullahi shugaban reshen kungiyar a jihar Oyo yace bisa ga tsarin kungiyar bana sun samu taimako daga sassa biyar na jihar sauran sassan kuma basu iso ba.

Daga sassan biyar da suka aiko da taimako sun samu Nera miliyan uku da dubu dari tara da sittin da takwas da dari takwas da hamsin.

A tsarinsu da kungiyar ta kasa ta tsara zaurawa da marayu da gajiyayyu ne za'a rabawa taimakon da suka samu. Misali sashin Ojo ya samu kudi dubu dari biyar. Cikin kudin sun ba marayu dari da tasa'in da biyar, sun baiwa zaurawa talatin da biyu kana sun ba gajiyayyu hamsin da hudu.

Ijnji Shaikh Abdullahi sun taimakawa marayu dari tara da hamsin, zaurawa kuma dari da tasa'in da shida, gajiyayyu kuma dari da arba'in da hudu.

Baicin kudaden da aka raba an kuma raba atamfofi da yaduka da shinkafa. Akwai ma wani sashen da ya dauki nauyin marayu saba'in na makarantarsu da ciyarwarsu da komi kama daga farkon karatu har su haye zuwa jami'a.

Acewar Shaikh Abdullahi aikin taimako wani aiki ne dake da tarin albarka. Misali duk wanda ya taimakawa maraya zai tashi kafada da kafada da Manzon Allah ranar tashin kiyoma.

Wasu da aka rabawa kyautukan sun nuna godiyarsu tare da jin dadi.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar IZALA Reshen Jihar Oyo Ta Tallafawa Zaurawa, Marayu da Gajiyayyu - 2' 59"