Shiek Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izala ta kasa a Najeriya, a wata zantawa da yayi da shashen Hausa na Mauryar Amurka, lokacin wata ziyara da suka kai kasar Amurka. Ya bayyana irin gudunmawar kungiyar su ga matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya bayyana cewar sukan gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari don bashi shawarwari akan hanyoyin da za’abi don kawo karshen kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram, da ma mayakan dake sace jama’a don neman kudin fansa a jihohin Zamfara, Kaduna harma da Katsina.
Ya kara da cewa kungiyar ta su a mtsayin kungiya mai zaman kanta ba kungiyar siyasa bace, amma sukan duba cancanta wajen zaben shugabannin, da kuma umurtar magoya bayansu akan wanda zasu zaba, ya kara da cewa ko a gaba idan ‘yan takara suka tsaya zasu duba don ganin wanda ya cancanta a zaba da kuma kira ga dukkan musulman Najeriya da su zabi wanda kungiyar ta aminta da shi.
Your browser doesn’t support HTML5