Badakalar kudade miliyan dubu dari biyu na Sefa da ake zargin wasu hukumomin Jamhuriyar Niger sun fitar zuwa waje bayan sun sayar da ton dubu biyar na ma’adinin uranium cikin wani yanayi mai daure kai ya sa kungiyar ITIE ta ladaptar da kasar.
Kungiyar ta kuma zargi kasar ta Niger da laifin hana yankunan da aka samo ma’adinan cin gajiyar abun da Allah ya basu domin su inganta rayuwarsu kamar yadda yarjejeniyar da suka yi ta tanada. Kamata yayi gwamnati ta dinga ba kananan hukumomin da ake hako ma’adinai a yankunan su domin taimakawa talakawa.
Ministan Ma’adanai na Niger Hassan Baraje ya yiwa ‘yan jarida bayani. Ya ce kungiyar ITIE bata yi anfani da rahoton da suka bayar ba na shekarar 2014 amma sai suka dogara kan rahoton kamun da aka yiwa wasu farar hula suka alakantashi da kokarin hanasu magana akan sayarda uranium din da ake baru akai. Y ace kungiyar ta zargi Niger da hana farar hula ‘yanci.
Sai dai gwamnatin Niger na ganin ba’a yi mata adalci ba wajen daukan matakin ladaptar da ita saboda haka ta dauki matakin da take ganin shi ne mafi a’ala gareta. Ministan yace Niger ta rubuta wasikar ficewa daga kungiyar gaba daya.
To sai dai wani dan majalisar dokokin kasar na ganin ficewa daga kungiyar wata guntuwar dabara ce saboda, inji shi kasar ba zata iya zama saniyar ware ba. Akwai kasashen da kasar ke muamala dasu cikin kungiyar saboda haka ficewa nada illa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5