Kungiyar ta ISIS, ta dauki alhakin wani harin bam da ya kashe gwamnan Lardin Aden a kudancin kasar Yamal tare da wasu da yawa daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
WASHINGTON DC —
Harin ya kaikaci jerin gwanon motocin Gwamna Gaafar Mohammed Sa’ad ne, yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa ofis a birnin Aden a jiya Lahadi.
Birnin na Aden, ya kasance filin daga a kasar ta Yamal, inda ‘yan tawayen Houthi suka karbe ikon Sana’a a bara kafin su doshi Aden, inda suka tilastawa Shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi yin hijra zuwa Saudiyya, wanda sai a watan da ya gabata ne koma garin.
Wannan fada na Yamal ya kashe dubban mutane, kuma mafi yawancinsu fararen hula, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana kasar a matsayin wacce al’umarta ta fada mawuyacin hali.