Kungiyar ISIS Ta Fille Kan Wani Ba Amurke Mai Aikin Agaji A Syria.

Alamun kungiyar ISIS.

A wani hoton vidiyo da aka sa a dandalin yanar gizo a yau Lahadi, yan yakin sa kan kungiyar ISIS sunyi ikirarin cewa sun file kan wani Baamerike ma'aikacin agaji mai suna Abdul Rahman Kassig.
Mai magana da yawun hukumar tsaro Bernadette Meeham, tace jami'an leken asiri suna aikin tantance sahihanci hoton vidiyon da ya nuna wanda aka ce an file kansa
Shi dai wannan mutumin dan shekara ashirin da shidda da haihuwa, tsohon soja, watani goma sha uku da suka shige aka sace shi a lokacinda yake gudanar da aiyukan taimako na jin kai a kasar Syria da yaki ya daidaita.
Iyalinsa sun fada cewa ya Musulta a lokacinda aka sace shi, ya canja sunasa daga Peter.
A kwanan nan Paula Kassig, yar uwar Baameriken da aka sace, ta fadawaToday wani shirin gidan talibijin na NBC cewa wasu yan makoni da suka shige an aiko wa ita da mijinta wani sako da aka dauka akan faifai da muryar shi Peter wanda ya canja sunasa zuwa Abdul Rahman yana fadin cewa lokaci yana kure masa.
Mutane uku da aka file kawunansa da aka nuna ta hoton vidiyo sun harda harda wani dan jarida Baamerike mai suna James Foley da Steven Sotlof wani dan Jarida Bamaerike dan asalin Isira'ila da kuma wani baturen Ingila ma'aikacin agaji mai suna David Haines.