Kungiyar ISIS Na Iya Yin Anfani da Makamai Masu Guba

Mutanen Mosul da suke layi domin karbar abincn da gwamnatin Iraqi take ba wadanda yakin ya yashesu kakaf

Fargabar da ake ji na cewa mayakan ISIS dake kokarin ci gaba da rike birnin Mosul na kasar Iraq a hannunsu karshenta zasu nemi anfani da makamai masu guba, na dada haifar da zaman dar-dar na irinwata gagarumar masifa da al’ummar yankin zasu abka a cikinta.

Duk da kokarin da sojan Iraq ke yi na neman fitarda mutane daga wasu sassa na garin Mosul din, har yanzu akwai dubban dubatan mutanen da ke cikin garin da wannan tarzomar ta rutsa da su.

Haka kuma duk da cewa sojoji suna da kayan aiki dake kare su daga makamai masu guba, ba wasu matakai masu inganci da aka dauka na kare fararen hula daga irin wadanan makaman.

Belkis Wille, wacce itace babbar jami’ar gudanarda bincike ta kungityyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tace ba wata cibiya – ko ta sojan Iraq ko ta Amurka ko ta wata kungiyar bada agaji – dake baiwa jama’a wani bayani kan abinda ya kamata suyi idan an kawowa garin farmaki da irin wadanan makaman masu guba.