Mayaka da sauran mabiya kungiyar ISIS, wadanda rushewar da daularsu ta yi a Siriya da Iraki ba ta sa sun karai ba, na dada karfi da kuma zama masu hadari, bisa ga wani binciken da jami’an bangaren yaki da ta’addanci na Amurka su ka yi.
Yayin da ba a bayyana dalla-dallar tsananin da barazanar ke yi ba, sabon binciken ya gano canjin da aka samu bai da nasaba sosai da dada karfi da ISIS ta yi kwanan nan kamar yadda yake da nasaba da tsarin da su ka yi wanda suke aiwatarwa sannu a hankali.
“Kungiyar ISIS ta yi ta kokarin sake farfado da karfinta na iya gudanar da ayyukanta,” abin da wani jami’in yaki da ta’addanci na Amurka ya gaya ma Muryar Amurka kenan. Ya kara da cewa, “Sun dada ingantawa tare kuma da sake fasalin yadda suke gudanar da harkokinsu ta yadda ya dace da yanayin inda su ke musamman ma a gabashin Siriya cikin tsawon watanni.”