Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wani hari a yankin Menaka da ke arewa maso gabashin kasar Mali a makon jiya, inda ta ce ta kashe sojoji 16.
washington dc —
Hukumomin gwamnatin Mali ba su yi magana kan lamarin ba tun bayan da aka fara samun rahotannin hakan a ranar 3 ga watan Agusta.
A dandalinta na farfagandar mai suna Amaq, kungiyar IS ta ce mayakan da ke da alaka da ita sun yiwa wa ayarin sojojin Mali da ke tafiya zuwa Nijar kwanton bauna .
Sojoji da dama sun jikkata, kuma an kwashe kusan sa'a guda ana gwabza fada, in ji kungiyar.
Tun a shekara ta 2012 ne kasar Mali ke fama da hare-haren mayakan IS da suka fara daga arewacin kasar zuwa tsakiyar kasar da ma makwabtan Burkina Faso da Nijar.
Rahoton na Human Rights Watch na baya-bayan nan ya zargi kungiyar ta IS da alhakin mace-macen “daruruwan mutane” tare da tilastawa dubbai barin gidajensu tun farkon wannan shekarar.