Kungiyar Hadin Kan Musulmai da Kiristoci Tayi Taron Zaman Lafiya da Juna A Abuja

Wasu musulmai da suke harabar wani masallaci

Kungiyar dake da cibiya a Kaduna ta shirya taron ne a Abuja wanda ya samu halartar dimbin mutane daga sassan Najeriya daban daban da suka koma gida don sanar da sakon aminci da salama bayan taron.

Imam Nureni Ashafa shugaban kungiyar ta bangaren lamuran Musulunci yace sun ga sakamakon abun da ya faru a Rwanda kuma wadansu sun fara kamun irin wannan ludayin a Najeriya.

Nufin irin wadannan 'yan Najeriyan da suka fara bin sawun abun da ya faru a Rwanda shi ne raba kawunan talakawan Najeriya baki daya, talakawan da yunwarsu iri daya ce, kukansu iri daya ne, lafiyarsu iri daya ce, damuwarsu iri daya ce, kana kasuwa daya suke zuwa cefane. Asibiti daya suke zuwa kuma 'ya'yansu makarantu iri daya suke zuwa.

Imam Ashafa yace wannan rin kamun ludayin zasu yi hobasa su nemi shugabanni su tabbatar 'yan Najeriya suna tare da dangantakar nan da aka sansu dasu da ita su kuma gina a kanta.

A nashi bangaren Pastor James Wuye na bangaren Kiristoci yace yana ji a jikinsa taron zai kawo sulhu mai dorewa tsakanin al'umma. Yace idan manufar kungiyarsu ta samu karba za'a so ta hayayyafa ta yadda duk kasar gaba daya a fara tattaunawa akan dangantaka da cudanya da juna. Yace duk wanda ya kasance a taron an sauya mashi tunane. An canza mashi alkibla. Ya gane yanzu cewa dama can mallakar hankalinsa a keyi. Matasa da yawa sun gane kuma sun lashi takobin cewa ba zasu yadda a sake yin anfani dasu ba.

Imam Ashafa da Pastor Wuye na cikin mutanen da rigingimun addini suka shafa a Kaduna. Amma maimakon rigingimun su barsu da tabon kiyayya sai suka zama sanadiyar fahimtar juna tsakaninsu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Hadin Kan Musulmai da Kiristoci Tayi Taron Zaman Lafiya da Juna A Abuja - 2' 21"