Kungiyar hadin kan matasan Afrika UPJ ta gudanar da wani taro a birnin Khartoum da ke Sudan, sakamakon ci gaba da bai wa dakarun sojojin kasashen waje wurin zama a Afrika.
Hakan ya sa kungiyar UPJ ta tuntubi shugabannin matasa na Afrika domin tattaunawa da kuma samun matsaya daya akan neman amsoshi na dalilin da ya sa dakarun ke ci gaba da zama a kasashen Afrika inda suka yi zargin shimfida ce ta dawo da mulkin malaka.
Aliyu Umarou, shugaban UPJ ya ce ba su yarda da sulhun da aka yi da su ba dalilin da ya sa suka yi shawarar fara rubuta takadar kara, da ta sanarwa domin a gane cewa dakarun sojoji da ake ta turawa Afrika ba su zo don aikin zaman lafiya ba.
Ana gudanar da taron Kungiyar UPJ ko wace shekara inda ake sauya waddanda suke jagorantar kungiyar. Matasan sun yi magana akan kwararar matasa zuwa kasashen turai ta barauniyar hanya, da matsalolin da yake sa matasan hijira.
Ga cikakken rahoton da Sule Moumouni Barma ya aiko mana kan wannan daga Nijar
Your browser doesn’t support HTML5