Yayinda suka fara taron shugaban kungiyar gwamnonin wanda kuma shi ne gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana jindadinsu da yadda bangaren shari'ar kasar ke gudanar da aikinsa musamman hukuncin da suka yanke a jihohin Akwa Ibom da Rivers.
Dangane da zabukan da za'a yi a jihohin Bayelsa da Kogi yace jam'iyyarsa ta samarda 'yan takara nagari wadanda zasu cire kitse a wuta lokacin zabukan..
Gwamna Okorocha yace sun amince da shugabancin Muhammad Buhari suna kuma jinjina masa da yadda yake gudanar da milkin kasar. Sun kuma kara jinjina masa da fafutikar da yake yi da cin hanci da rashawa da kuma kokarinsa na shawo kan matsalar tsaro.
Mai masaukin baki gwamnan jihar Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya yi tsokaci akan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki da kuma matakan da ya kamata a dauka domin a farfado dashi. Yace akwai bukatar a soma duba cikin gida wajen samarda kudaden shiga aljihun gwamnati kada a cigaba da dogaro ga kudin man fetur.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5