Kungiyar ta G5 Sahel, ta kunshi kasashe ne da suka hada da Mali, da Bukina Faso, da Niger da Chadi da kuma da Murtania.
Yanzu haka kungiyar tana gudanar da taron ta zagaye na hudu tun bayan da kasashen suka kafa rundunar hadin gwiwa da zummar yaki da kungiyoyin taaddancin da suka mamaye arewacin Mali, kuma suke kai hare-hare a kasashe makwabta irin su Nijar da Bukina Faso.
Taron wanda ake gudanarwa yau,yazo dai-dai da lokacin da shugaban ta na farko, shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Keita, ke kammala waadin shugabancin sa na Kungiyar.
Daya daga cikn abinda taron na yau zai baiwa fifiko shine batun hada kai domin samun zaman lafiya da cigaban kasashen na yankin Sahel.
Shugaban na Mali yace haka kuma zasu ci gaba da karfafa ayyukan cigaban karkara, samar da aikin yi ga matasan kasashen su, da batun samar da makamashi.
Ga Sule Mumuni Barma da Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5