Wata kungiyar da take kare hakkin Fulani, musamman makiyaya da ake kira ‘kautal hore’ ko hada-kai, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike kan harin da aka kai wa Fulani wanda ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi a tsaunin Mambilla dake jahar Taraba.
Shugaban kungiyar kautal reshen jihar Bauchi, Alhaji Mohammadu Husseini Buzaye, wanda ya yi wannan kira, ya ce an dade ana ce masu za a gudanar da bincike amma shiru ake ji.
Kungiyar kautal mai kare ‘yancin Fulanin, ta gudanar da taro ne a yankin karamar hukumar Toro a jahar Bauchin, domin auna halin da Fulani suka sami kansu a ciki, da kuma duba shirin bude kasuwannin-shanu a arewacin Najeriya, maimakon jigilarsu zuwa kudu.
Shugaban kungiyar a shiyyar arewa maso gabas Alhaji Hashim Abubakar, ya ce bude kasuwannin ya zama wajibi ganin matsaloli da suke tattare da jigilar dabbobi zuwa kudancin Najeriya.
Shugabannin sun yi zargin cewa masu shanu suna kashe rabin kudin saniya guda kafin su isa kudancin Najeriya, saboda haka suka ce, wasu Fulanin ba sa iya dawowa arewa, bayan sun sayar da dabbobinsu.
Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5