To sai dai kuma gwamnatin mulkin sojan ta ki bin umarnin, maimakon haka ta zabi yanke alakar huldar diflomasiyya da Najeriya da sauran kasashen da ke goyon bayan dawo da Muhammad Bazoum kan karagar mulkin kasar.
Gwamnatin mulkin soja, a yanzu karkashin jagorancin kwamanda Janar Abdourahamane Tchiani, ta jajirce wajen yin tir da matsin lamba daga waje.
ECOWAS ta aike da wata babbar tawaga domin tattaunawa da shugabannin juyin mulkin tare da nufin shawo kan lamarin cikin lumana, amma tattaunawar ta hadu da cikas.
Tawagar karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai murabus, ta hada da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda ke rike da mukamin shugaban kungiyar kasashen ECOWAS, ya bukaci a sake wani babban taron koli na musamman wanda ake sa ran zai wakana a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, 2023, a Abuja.
Taron zai tattauna ne kan yanayin siyasa da kuma abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar da kuma samo hanya mafi sauki don shawo kan lamarin.
A yayin taron, shugabannin ECOWAS za su zurfafa nazari kan yanayin siyasa mai sarkakiya da kuma yin shawarwari kan matakin da za su dauka.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta jaddada muhimmancin wannan tattaunawa dangane da abubuwan da ke faruwa a Nijar.
Yayin da lamarin ke kara ta'azzara, kasashen duniya za su ci gaba da sa ido domin ganin sakamakon wadannan muhimman shawarwari da matakai da kungiyar ECOWAS za ta dauka.
~ Yusuf Aminu Yusuf