Kungiyar Dillalan Man Fetur Ta IPMAN A Najeriya Ta Shiga Yajin Aikin Gargadi

Karancin man fetur a Najeriya.

Wannan yajin aiki ka iya haifar da matsalar karancin man a yankin arewacin kasar ciki har da Abuja, babban birnin Najeriya kamar yadda masu lura da al'amura suka bayyana.

Kungiyar dillalan man fetur shiyyar arewacin Najeriya, ta fara yajin aikin kwana uku.

Yajin aikin wanda ta fara a ranar Litinin na matsayin gargadi ne ga hukumomi kan wasu kudade da mambobin kungiyar ke bin gwamnatin Najeriya.

Rahotannin sun yi nuni da cewa kungiyar ta janye motocin da ke dakon kayan mai a depo-depo da ke sassan arewacin kasar.

Kungiyar tana ikirarin cewa tana bin gwamnatin sama da Naira biliyan70 da take dauko man daga kudancin zuwa arewacin Najeriya.

Bayanai sun yi nuni da cewa, gwamnati ta ba kungiyar Naira biliyan biyu, bayan da kungiyar ta nuna matsalin lamba kan a biya ta kudadenta.

Ku Duba Wannan Ma Masana Harkar Man Fetur Na Ta Mahawara Kan Yiwuwar Magance Karancin Man Fetur

“Ba wata daya ko biyu ba, wani wata tara yake bin kudaden, kowa abin ya ishe shi.” In ji Alhaji Muhamamed Kolo, shugaban kungiyar a jihar Borno.

Wannan yajin aiki ka iya haifar da matsalar karancin man a yankin arewacin kasar ciki har da Abuja, babban birnin Najeriya kamar yadda masu lura da al'amura suka bayyana.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, gwamnatin tarayyar tana ikirarin cewa ba ta da kudi ne a hannunta.

Mambobin kungiyar dillalan man kan yi dakon man fetur din ne daga depo-depo na mai da ke kudancin zuwa arewaci, sannan daga bisani gwamnati tarayyar ta biya su kudin dakon.

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Dillalan Man Fetur A Najeriya Ta IPMAN Ta Shiga Yajin Aikin Gargadi 3'48" .mp3