Sanarwar da rundunar ta fitar ta sa mutane da dama cikin farin ciki yayin da wasu kuma ke tababan ikirarin.
Amma a 'yan kwanakin nan kungiyar dattawan jihar Borno ta kira wani taron manema labarai a fadar gwamnatin tarayya, wato Abuja inda suka yabawa sojojin dake jihar Borno. Sun yaba masu da irin ayyukan da suke yi. Sun umurci sojojin da su dauki wasu mutane da 'yan jarida su ziyarci wuraren da suka kwato domin tabbatar da ikirarin jami'an tsaron.
Mamaye garuwan da 'yan bindigan suka yi yayi sanadiyar mutane da dama sun rasa muhallansu musamman mata da yara. Manyan birane dai na cike da 'yan gudun hijira wadanda aka kwace kauyukansu.
Ganin ya kamata sojoji su tabbatar da sahihiyar gaskiyar lamarin sun soma fitar da hotunan kauyukan da suka kwato domin mutane su gamsu. Sun nuna wasu motocin soji da 'yan Boko Haram suka kwace can baya wadanda ma suna dauke da tambarin Boko Haram din.Sojojin na nuni cewa sun sake kwato kayansu.
Sun kuma nuna wasu 'yan Boko Haram din da suka yi shigen mata domin su batar da kama, su samu su tserewa jami'an tsaro.
Wasu 'yan jihar sun ce wani lamari ne da suka dade suna jira sai gashi Allah ya kaddara an soma kwato garuruwan. To saidai jama'a na tambaya. Shin me ya sa gwamnatin tarayya bata dauki matakan da suka dace ba sai yanzu. Kodayake wasu mutane na fasara lamarin ta fannin siyasa wasunsu kuma suna murnar cewa an soma samun galaba akan 'yan ta'ada.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5