Kungiyar Daliban Najeriya, NANS Ta Yi Barazanar Shiga Kafar Wando Daya da Gwamnati

Daliban Najeriya

Kungiyar daliban Najeriya ta ba gwamnatin Najeriya kwanaki ishirin da daya ta warware rikicinta da kungiyar malamansu wato ASUU , idan kuma ba hakan ya faru ba zasu dakatar da duk ayyukan gwamnati a duk fadin kasar,

Kungiyar dalibai ta kasa ko NANS ta dora laifin abun da ya haddasa yajin aikin malamansu akan 'yan siyasa da suka zarga da son kansu da yin shakulatin duk wani abu da bai shafesu ba.

Kungiyar ta ba gwamnatin tarayyar Najeriya kwanaki ishirin da daya da ta sasanta da malaman ko kuma su daliban su sa kafar wando daya da gwamnati. Kungiyar ta yi barazanar tsayar da harkokin gwamnati idan har wa'adin da suka bayar ya cika ba'a yi komi ba.

A jami'ar Legas wasu dalibai sun bayyana yadda yajin aikin ya shafesu. Wani Umar Usman Askira yace su dalibai basu ji dadin yajin aikin ba saboda jadawalin jarabawa ya fito da zasu fara ranar 28 na wannan watan.

Daliba Adefemi tace da safe aka gaya masu babu koyaswa, babu jarabawa ko bincike saboda malaman sun shiga yajin aiki. Kamar Umar, tace bata ji dadin yajin aikin ba.

A martanin farko da gwamnati tarayya ta fitar ma'aikatar ilimi ta bakin kakakinta tace gwamnati na tattaunawa domin gano bakin zaren rikicin,

Ga rahoton Banagida Jibrin da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Daliban Najeriya, NANS Ta Yi Barazanar Shiga Kafar Wando Daya da Gwamnati - 2' 59"