Malam Jibo Mamman mai ba kungiyar shawara shi ya bayyana cewa mutane basa ganin aikin kungiyar dalili ke nan da ake samun cikasa.
Inji Jibo Mamman ya kamata duk dokokin da suka shafi cin hanci da rashawa ko wani kokarin yin almundahana yakamata a tattarasu cikin kudu guda domin a dakile yadda dokokin ke karo da juna.
Dalili ke nan da suke ziyara jiha jiha suna fadakar da jama'a da masu yin dokoki da masu fada a ji su fahimta su san dalilin da suke son a hada dokokin wuri guda.
Kungiyar ta gana da kungiyoyi da dama da suka hada da kungiyin fararen hula da zummar kawo fahimtar juna.
To amma Malam Saidu Alher na gamayyar kungiyoyin fararen hula na cewa an yi tuya an manta da albasa domin taron bai kamata ya sayan 'yan siyasa da wakilan kungiyoyin fararen hula ba kawai ba. Yace ya kamata a tattaro jama'a su ji su fahimtu.
Ga rahoton Mamman Haruna Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5