Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tace zata dawo cigaba da wasannin firimiya lig, ba tare da wasu manyan 'yan wasanta ba, sakamakon rauni da suka samu a wasannin da suka fafata wa kasashen su.
A ranar Asabar 19 ga watan Oktoba 2019 Chelsea zata kara da Newcastle United cikin gasar firimiyan Ingila mako na Tara.
Kocin kungiyar Frank Lampard ya ce 'yan wasa irin su N’Golo Kante, Andreas Christensen, duk kansu suna fama da rauni a wasan da suka fafata na kasa-da-kasa, sai Mateo Kovacic.
Reece James shima ana tsammanin ba zai buga wasan ba, inda ake sa ran 'yan wasa Emerson Palmieri da Antonio Rudiger suna daf da dawowa buga wasanni bayan sunyi fama da jinya.
Sai dai maihoras da kungiyar ta Chelsea Lampard, ana tsammani zai yi amfani da Fikayo Tomori da Kurt Zouma, a matsayin masu tsaron baya daga tsakiya.
Shi kuwa jagoran 'yan wasa wato (Captain) Cesar Azpilicueta zai buga gefen dama na baya akwai kuma Marcos Alonso Jorginho a tsakiya.
Ana sa ran Ross Barkley zai samu shiga, ganin yadda ya samu kansa a wasan da Ingila suka kara da takwararta kasar Bulgaria.
Cikin jerin 'yan wasan akwai Callum Hudson-Odoi wanda ya murmure daga raunin da ya samu kafin tafiya wasannin kasa, haka zalika Tammy Abraham shi zai jagoranci tawagar a gasar ta ranar Asabar, inda zasu buga tsarin wasa na (4,3,3).