Kungiyar kwallon kafar Chelsea ta samu nasarar cin kofin Europa, biyo bayan lallasa Arsenal da tayi da kwallaye 4-1, a wasan karshe da suka fafata a birnin Baku na Azerbaijan.
An shafe zagayen farko na wasan ana ta kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin biyu ba tareda jefa kwallo ko tilo ba.
A mintuna na Arba'in da tara ne, wato jimkadan bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci, tsohon dan wasan Arsenal wanda kuma yanzu haka ke takawa Chelsea leda, Giroud ya jefa kwallon farko a ragar tsohuwar kungiyar tasa ta Arsenal.
Pedro ne yaci kwallo ta biyu wa Chelsea, yayin da Eden Hazard ya kara ta uku ana minti 65 da fara wasa.
Alex Iwobi ne ya jefawa kungiyarsa ta Arsenal kwallo daya tilo data samu, kafun daga bisani Eden Hazard ya jefa kwallo ta hudu a ragar Arsenal, wanda hakan ya bai wa kungiyarsa ta Chelsea damar lashe gasar.
Wannan shine karo na biyu da kungiyar ta Chelsea ke lashe gasar ta Europa bayan da ta lashe na farko a 2013.
Wannan kuma shine kofi na farko da Sarri ya dauka tun da ya fara horasda kungiyar ta Chelsea a 2018.
Rabon da Arsenal ta lashe kofin Europa tun a shekarar 1994. Rashin nasarar da Arsenal din tayi jiya na nufin cewa, ba zata samu daman shiga cin kofin zakarun turai na kaka mai zuwa ba.