Kungiyar Chelsea Ta Shigar Da Karar Kungiyar FIFA

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta daukaka kara ga hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA kan dakatar da ita da tayi daga sayen matasan 'yan kwallo kafa har na tsawon shekaru biyu.

A kwanakin bayane hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da Chelsea daga sayen sababin 'yan wasa, saboda samunta da karya dokokin daukar matasan 'yan wasa da kulob din yayi.

Hukumar ta ce an karya doka a kan sayen 'yan wasa har guda 29 daga cikin 92 da kungiyar ta saya.

Dakatarwar ba zai hana Chelsea sayar da na ta 'yan wasan ba, kuma ba zai shafi kungir kwallon kafa na mata ba, da kuma ta kwallon kafar Futsal ba, wato masu taka leda a rufaffen daki.

Har ila yau kuma FIFA, ta ci tarar kungiyar ta Chalsea kudi har fam dubu 460,000 tarar ta hada da hukumar kula da kwallon kafar Ingila ta FA inda FIFA taci tararta fam dubu £390,000.

Haramcin ya zo ne bayan wani bincike da FIFA ta yi a kan wasu matasan 'yan kwallo da Chelsea ta saya, har da tsohon dan wasan gabanta Bertrand Traore.

In har Chelsea batayi nasara akan daukakaka karar da tayi ba, to ya tabbata bazata sake sayen sababin 'yan wasa ba har sai shekara 2020.