Kungiyar Chelsea Ta Dauki Sabon Koci Frank Lampard

Sabon kucin kungiyar Chelsea Frank Lampard

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bada sanarwar daukan Frank Lampard a matsayin sabon kocinta.

Lampard tsohon dan wasan kungiyar ta Chelsea wanda ya shafe shekaru 13 yana taka leda, ya maye gurbin Maurizio Sarri ne wanda ya bar kungiyar a watan Yuni 2019, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus a kasar Itali a matsayin mai horas da ita.

Chelsea ta kulla yarjejiniyar shekaru uku da Frank Lampard, tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea Lampard mai shekaru 41 da haihuwa dan asalin kasar Ingila ya fafata wa Chelsea wasanni 648, ya samu nasarar daukan manyan kofuna 11.

Kafin zuwansa Chelsea a matsayin mai horas da 'yan wasa, Lampard ya jagoranci kulob din Derby County, ya karbi kungiyar ta Chelsea a wani hali da take ciki, wanda hukumar kula kwallon kafa ta duniya FIFA ta haramta mata sayen 'yan wasa har na tsawon shekaru biyu, sakamakon laifin da ake tuhumarta dashi na sayen matasan 'yan wasa 'yan kasa da shekaru 18, sai dai ta daukaka kara a kan hukuncin da akayi mata.

Lampard ya bayyana jin dadinsa yadda ya koma tsohuwar kugiyarsa da ya bugama kwallo, a yanzu kuma shine mai horas da ita.

Yayi alkawarin yin aiki tukuru don kawo canji mai kyau a kungiyar, inda ya gode wa jagororin kungiyar bisa wannan damar da aka bashi.