Kungiyar hadin kan kirista a Najeriya wato CAN a takaice, ta shirya gudanar da addu'o'i na kwanaki uku a fadin Najeriya don rokon Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.
Wannan kiran na zuwa ne bayan wasu hare hare da kashe kashe da 'yan bindiga su ka yi kwanan nan a wasu yankunan kasar.
Sakataren Kungiyar CAN a jihar Filato, Rabaran Polycarp Lubo ya ce komawa ga Allah shi ne mafi a'ala wajen magance matsalolin tsaro a kasar.
Shi ma Shugaban majami'ar ECWA ta kasa da kasa, Rabaran Stephen Panya Baba, ya ce jama'a na cike da bakin cikin kashe-kashe, da satar mutane don neman kudin fansa da sauran ayyukan ta'addanci da ke faruwa a kasar.
Limamin darikar Katolika a Abuja, Arch Bishop Ignatius Kaigama, ya yi kira ga masu aikata ta'asar akan su tuba.Ya ce su ajiye makaman su domin ranar shari'a na zuwa.
A saurari rahoto cikin sauti daga jihar Filato.
Your browser doesn’t support HTML5