Kungiyar CAF Bata Adalci Wajen Zaben Zaratan Nahiyar Afrika

Tsohon dan wasan Najeriya Emmanuel Amunike

Tsohon dan wasan Super Eagles,na tarayyar Najeriya, kuma mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Tanzania Emmanuel Amunike, ya nuna rashin jin dadin sa bisa gazawar da ‘yan wasan Najeriya ke yi, wajen lashe kyaututtukan da hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF take bayarwa a duk shekara.

Tsohon dan wasan Amunike yace ya dace ‘yan Najeriya su farga su gane cewar, sun shafe shekaru da dama basa samun kyakkyawar wakilci a duk lokacin da hukumar CAF ke gudanar da bukukuwan karrama ‘yan wasa. Kungiyoyin kwallon kafa, da kuma bangaren masu horarwa a nahiyar Afrika.

Inda a ranar Talata 9/1/2019 Najeriya ta samu kyauta daya kacal daga CAF na kungiya mafi kwazo a kwallon kafa, na Afrika bangaren Mata.

Rabon Najeriya da ta samu wani babbar kyauta tun tsohon dan wasanta Kanu Nwankwo, da ya lashe gwarzon shekara a shekarar 1999 shekaru ashirin baya.

Shi kuwa wani tsohon dan wasan tsakiya na Najeriya Edema, wanda ya fafata a wasan da Super Eagles suka lashe kofin gasar Afrika a shekarar 1994, ya ce akwai gyara kan tsarin da hukumar CAF take bi wajen zaben gwarzon dan wasan nahiyar Afrika.

Dan wasan yace ya kamata hukumar ta dinga zaben gwarzon ne da ga cikin gasar da take shiryawa kawai, ba tare da ta hada da kokarin da dan wasa yayi a wasannin kasashen Turai ba.

Ta hakane kawai CAF za ta rika yi wa ‘yan wasan da ke buga gasannin nahiyar Afrika adalci, amma ba a koda yaushe a rika karrama ‘yan wasan da ke buga gasannin nahiyar Turai ba.