Kungiyar Brighton Ta Kori Mai Horar Da Ita

Christopher Hughton

Kungiyar kwallon kafa ta Brighton and Hove Albion FC ta kasar Ingila ta sallami mai horar da ita, Christopher Hughton, bayan da ya shafe shekaru hudu da rabi a kulab din, a cewar wata sanarwa a jiya Litinin.

Hughton ya jagoranci kungiyar da ya dagota da ita a shekarar 2017, wacce kuma ya kawo karshen matakin shekaru 34 da suka yi suna buga karamar gasa.

Hakan ya ba su damar tsira a wannan kakar wasannin ta biyu da suka buga duk da irin rashin nasara da suka yi a duka wasaninsu na karshe guda 9.

“Babu shakka, wannan wani mataki ne mai matukar wahala da ya kamata na yanke a matsayina na shugabana kungiyar Brighton and Hove Albion." Inji shi.

“Amma a karshe, dole na yi, saboda yadda muka rika fama da matsaloli a zagaye na biyu a wannan kakar wasannin." ya kara da cewa.