Kungiyar Boko Haram Kai Hari Cikin Wasu Unguwannin Maiduguri

Mutanen da suke gudu daga harbe harben 'yan Boko Haram

A lokacin da ake sa ran an shawo karfin 'yan Boko Haram sai gashi jiya sun kai hare-hare a wurare da dama cikin birnin Maiduguri lamarin da ya jefa jama'ar garin cikin wani halin kakanikayi

Tun daga misalin karfe biyar na maraicen jiya ne wasu 'yan Boko Haram suka farma wasu unguwannin cikin garin Maiduguri wanda hakan ya tada hankulan jama'a kowa ya kama gudun idan baka yi ka bani wuri.

Mutane da yawa suka fice daga gidajensu domin gudun abun da ka kai ya komo. Mutanen unguwannin bazuwa suka yi yayinda wasunsu basu san inda suka nufa ba. Yawancin mutane sun kidime saboda rashin sanin tabbas.

Muryar Amurka ta ga mata da yara suna takawa da kafa a kan tituna saboda rashin ababen hawa ko kuma duk wani abun hawa da ya fito daga unguwannin cike ake ganinsu da jama'a. Mata da yara dai sai yawo suke suna neman wurin fakewa.

Jami'an tsaro na sintiri suna kai da kawowa saboda yadda hankali mutane ya tashi tare da fadawa jama'a su kwantar da hankali domin sun shawo kan duk abun dake faruwa

Wasu daga unguwannin Polo da Bolori da aka tambayesu inda zasu sun ce basu sani ba. Suna dai tserewa ne saboda karar bamabamai. Wasu ma suna rike da takalmansu ne.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Boko Haram Kai Hari Cikin Wasu Unguwannin Maiduguri - 2' 57"