Kungiyar Boko Haram Ta Kai Hari Yankin Madagali Jihar Adamawa

Wasu da suka gudu daga gidajensu

Wasu da suka gudu daga gidajensu

Kungiyar Boko Haram ta sake kai hari yankin Madagali cikin jihar Adamawa karo no hudu cikin wata guda inda ta haddasa asarar rayuka da dukiya
'Yan kungiyar Boko Haram sun kai har a yankin Madagali karo na hudu cikin wata guda.

Harin baya-bayan nan sun kai ne akan kauyen Kubla dake cikin karamar hukumar Madagali wadda ke makwaftaka da jihar Borno. Al'ummar yankin sun kwana cikin zullumi. Kawo yanzu ba'a san adadin mutanen da harin ya rutsa da su ba.

Wani dake kauyen yace mutane suna cikin barci sai aka dinga jin karar bindigogi. An yi musayar wuta tsakanin 'yan bindigan da sojojin dake kan iyaka tsakanin jihohin Borno da Adamawa. Sun kwana suna ta harbe-harbe domin 'yan bindigan nada yawa. Yan bindigan sun yi kone-kone, sun kuma kwashe kayan abinci kacokan.

Cikin 'yan kwanakin nan yankin na Madagali ya sha fama da hare-hare da 'yan Boko Haram ke kaiwa. Duk lokacin da suka kai hari ana samun asarar rayukan mutane da dama kuma mutane na ficewa daga gidajensu domin kare rayukansu.

Shugaban karamar hukumar Madagali Mr. James Abawu Wasadda yace mutane sun gudu daga gidajensu. Sai daga baya idan kura ta lafa wadanda suka rayu su dawo. Yanzu dai jama'ar garin sun bar gidajensu.

A can jihar Taraba dake makwaftaka da jihar Adamawa wasu mutane sanye da kayan sarki suka kai hari a garin Cinke dake yankin Wukari inda aka samu asarar rayuka da dukiya. Yan bindigan da suka shiga garin sanye da kayan sarki har da kayan 'yan sandan kwantar da tarzoma ana zaton jam'an tsaro ne amma sai suka budewa mutane wuta. Sun kashe mutane tara kuma sun kone gidaje kimanin guda dari. Wannan lamarin na zuwa ne bayan Jukunawa da Fulani da Hausawa sun raftaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Boko Haram Ta Sake Kai Hari Yankin Madagali Jihar Adamawa - 2' 36"