Wasu rahotanni daga mujallun kasar Spain sun bayyana cewar, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wadda ta lashe kofin gasar Laliga na bana, kuma karo biyu ajere, ta fara kokarin tantance sabon mai horaswa wanda zai maye mata gurbin kocinta na yanzu Ernesto Valverde.
Hakan ya biyo bayan ganin rashin tabbas na ci gaba da aikin Valverde, a matsayin mai horar da 'yan wasan nata wanda ya taimaka mata ta lashe kofin gasar La Liga na bana.
Sai dai duk da nasarar da ta samu a gasar ta LaLiga, Barcelona ta gaza lashe kofin gasar Copa del Rey, a karshen makon da ya gabata, inda Valencia ta doke ta daci 2-1, haka kuma kungiyar ta gaza kaiwa wasan karshe na gasar zakarun Turai, yayin da Liverpool ta lallasa ta daci 4-0, duk da cewa a zagayen farko, Barcelona ce ke jagoranci da 3-0.
Yanzu haka dai rahotanni sun ce kungiyar ta Barcelona ta jera sunayen wadanda take sa ran zaba ciki, su maye gurbin kocinta Ernesto Valverde, wanda suka hada da, Kocin Arsenal Unai Emery, kocin kasar Holland Ronald Koeman, Massimiliano Allegri, kocin Juventus da kuma tsohon kocin Everton Roberto Martinez, domin tun karar kakar wasannin shekara mai zuwa 2019/20.