Kungiyar Agaji Ta Red Cross Zata Zurfafa Taimakon Yankin Gaza

Wasu Ma'aikatan Kungiyar Red Cross da wani majinyaci a kwance a gadon asibiti.

Kungiyar bada agajin kasa da kasa ta Red Cross ta sanar a jiya Laraba 31 ga watan nan na Mayu cewa ta tura da Likitocin tiyata da wasu kwararrun jami’an kiwon lafiya tare da kayayyakin taimako domin taimakawa abin da ta kira “karuwar bukatar taimako a fannin lafiya a Gaza.

Kungiyar Red Cross tace karfafa taimako da zata yi na watanni shida, zai hada da kafa cibiyar tiyata mai dauke gadaje 50 don bada himma ga jinyar mutanen da suke fama da raunin harbin bindigar da aka samu a cikin wani tashin hankali na baya bayan nan a kan iyakar Isra’ila da Gaza.

Rundunar Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 115 tun daga karshen watan Maris zuwa yanzu, lamarin da ya janyo wa Isra'ila suka na yin amfani da karfa-karfa. Isra’ila ta zargi mayakan kungiyar Hamas da takalar tashin hankalin kuma tace ta dau wannan mataki ne domin kare kan iyakarta.

Tashin hankalin da ya barke a kan iyakar kasashen ya yi sauki a jiya Laraba, yayin da jami’an Falasdinawa suka ce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ira wadda Masar ta jagoranta.

Sai dai jami’an Isra’ila basu tabbatar da wannan yarjejeniyar ba, amma dai sun ce idan aka daina harbo harsashi ko roka daga Gaza inda mayakan sa kai suke, to Isra’ila ma zata dakatar da martanin hare-harenta.